1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayer Leverkusen ta kafa tarihi a kakar wasan Bundesliga

Mouhamadou Awal Balarabe
May 20, 2024

Bayer Leverkusen ta yi nasarar zama kungiya daya tilo da ta kammala kakar wasan Bundesliga ta Jamus ba tare da an doke ta ba, yayin da Manchester City ta kasance farau ta zama zakara sau hudu a jere a Premier League.

https://p.dw.com/p/4g4HW
Koci Xavi Alonso da 'yan wasan Leverkusen na murnar zama zakaran Bundesliga
Koci Xavi Alonso da 'yan wasan Leverkusen na murnar zama zakaran Bundesliga tare da kafa tarihiHoto: Michael Probst/AP Photo/picture alliance

'Yar baiwa Bayer Leverkusen ta sake nuna halin arziki a fagen kwallon kafa a karawarta ta karshe a kakar wasa ta 2023/2024 ta hanyar doke Augsburg da ci 2-1 a filin wasa na BayerArena. Ko da shi ke dai dama tana da tabbacin samun kambun zakara tun makonni biyar da suka gabata, amma wannan nasarar ta sa Bayer Leverkusen zama kungiya ta farko da ta kammala kakar Bundesliga ba tare da shan kaye ko sau daya ba , inda ta samu nasarori 28 da canjaras 6.

Karin bayani: Leverkusen ta zama zakarar Bundesliga 2024

Kungiyar da Xabi Alonso ke jagoranta ta tsawaita yawan wasanni guda 51 da ba ta baras ba a ciki da wajen Jamus tun bayan fara kaka, lamarin da ya faran ran koci inda ya ce: "Ina matukar alfahari da kungiyar da wasannin da suka gudanar. 'Yan wasa sun nuna da'a a duk tsawon kakar wasa. lashe gasar Bundesliga ba abu ne mai sauki ba, amma dai kwalliya ta biya kudin sabulu. Don haka, ina bukatar dan lokaci don yin nazari tare da sanin abubuwan da suka haddasa wannan nasarar."

Magoya bayan Bayer Leverkusen sun rinka kara wa 'yan wasansu kwarin gwiwa a tsawon kakar wasa
Magoya bayan Bayer Leverkusen sun rinka kara wa 'yan wasansu kwarin gwiwa a tsawon kakar wasaHoto: Wolfgang Rattay/REUTERS

Ita dai Leverkusen mai maki 90, ta yi wa Stuttgart da ke a matsayi na biyu ratar maki 17 bayan da ta mamaye Borussia Mönchengladabach da ci 4-0. Ita kuwa Bayern Munich ta yi abin kunya inda Hoffenheim ta lakaba mata dan karen kashi 4-2, saboda haka ne ta yi asarar matsayinta na biyu i zuwa na uku da maki 72. Amma a bangarenta Borussia Dortmund ta gasa wa Darmsatadt aya a hannu da ci 4-0,  gabanin wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai da Real Madrid a birnin London. A nata bangaren Union Berlin ta ceci kanta daga halin gangarawa karamin lig ta hanyar cin nasara a kan Freiburg da ci 2-1. Amma Köln ta bi sahun Darmstadt wajen yi ban kwana da Bundesliga bayan da sabon shiga Heidenheim ta mamaye ta da ci 4-1.

Manchester City ta zarta sa'a a Ingila


Manchester City ta zama zakaran kwallon kafar Ingila karo na hudu a jere sakamakon nasarar da ta samu a kan West Ham da ci 3-1. Ita dai wannan kungiyar da Pep Guardiola ke horaswa, sau uku kawai aka doke ta a kakar wasa ta 2023-2024, lamarin da ya sa ta samun kambu na shida a a shekaru bakwai, sannan 10 a tarihinta. Dadin dadawa ma, City ta zama kungiyar farko da ta zama gwana sau hudu a jere a Premier League.

Karin bayani: Labarin Wasanni: Sakamakon lig-lig a Turai


A daidai wannan lokaci, kocin Manchester City Pep Guardiola ya nuna shakku kan makomarsa a kungiyar bayan 2025, inda ya nuna alamun gajiya da kosawa bayan shafe shekaru takwas yana horas da ita. A Ingila dai, fitaccen kocin Manchester United Alex Ferguson ne kawai ya fi Pep Guardiola taka rawar gani, inda kungiyar da yake horaswa ta zama zakara sau 13 cikin shekaru 28, yayin da a karkashin Guardiola, City ta zama kungiyar farko na Ingila da ta lashe gasar Premier da kofin FA da na kalubale a 2019, kafin a 2023 ta lashe kofin zakarun Turai da kambun zakaran Ingila da kofin kalubale. A yanzu dai,Arsenal ce ke a matsayi na biyu da maki 89 yayin da Liverpool ke a matsayi na uku da maki 82 a teburin Premier League.

Kungiyoyin Masar sun mamaye kwallon kafa a Afirka

Zamalek ta Masar ta yi nasarar doke RS Berkane tare da lashe kofin CAF na Afirka
Zamalek ta Masar ta yi nasarar doke RS Berkane tare da lashe kofin CAF na AfirkaHoto: Abeer Ahmed/NurPhoto/picture alliance

Kungiyar Zamalek ta Masar ta sake lashe kofin CAF a gida birnin Alkahari bayan da ta doke RS Berkane ta Maroko da ci1-0 a mataki na biyu na wasan karshe, duk da rashin nasara da ta yi a wasan farko da ci 1-2. Wannan shi ne kambu na biyu a tarihinta ta Kungiyar ta birnin Alkahira ta lashe kofin Confedertion Cup ta Afirka, kuma tarihi ya maimata kansa domin ko a kakar wasa ta 2018-2019, a gaban Berkane ne Zamalek ta ciri tuta a karon farko. Dama dai rikici dflomasiyya da aka samu tsakanin Aljeriya da Maroko kan tsawirar yammacin Sahara ne ya sa CAF ba wa RS Barkane damar zuwa wasan karshe ba tare da ta yi wasa da takwarata ta Aljeriya ba.

Karin bayani: Wassani: Masar ta mamaye gasar wasannin Afirka

A gasar zakaru tanahiyar Afirka kuwa, Espérance Tunis da Al Ahly ta Masar sun tashi babu kare bin damo 0-0 a matakin farko na wasan karshe na gasar Champions League a birnin Radès. Kyakkyawar kora daya kacal aka samu a duka wasan saboda taka-tsantsan da kungiyoyin biyu na Tunisiya da Masar da sau shida suna karawa a wasan karshe suka yi.  A ranar 25 ga watan Mayu ne za a san maci tuwo tsakanin Misirawan Al-Ahly da ke zama ja gaban wajen lashe champions league na Afirka sau 11 da kuma 'yan Tunisiya wadanda ke fafata wasan karshe na kofin zakarun Turai karo na 9 a tarihinsu.

Usyk ya zama sabon shagon boxing na duniya

Oleksandr Usyk ya zama sabon shagon boxing na duniya
Oleksandr Usyk ya zama sabon shagon boxing na duniyaHoto: Richard Pelham/Getty Images

Dan kasar Ukraine Oleksandr Usyk ya zama sabon zakaran Dambe boxing na duniya ajin masu nauyi na WBC bayan da ya zarta Tyson Fury na Burtaniya da yawan maki a fafatawar da suka yi a daren ranar 18 zuwa 19 na Mayu a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. Wannan nasarar ta ba wa Usyk damar hade dukanin manyan kambun boxing na duniya kama daga na WBA da WBo da IBF, lamarin da rabon da ganin irinsa tun  shekaru 25 da suka gabata, lokacin da Lennon Lewis ya nuna irin wannan bajinta a shekara ta 2000 inda ya samu kambaya uku.

Tun dai a watan Oktoban bara ne bakin alkalami ya fara bushewa Tyson Fury, inda ya sha da kyar a hannun dan boxing na Kamaru Francis Ngannou, lamarin da ya jefa shakku kan makomar dan Birtaniyya da ya suna a fannin dambe a duniya. Sau 34 ne Fury ya samu nasara wasu lokutan ma kafin a kai karshen turmin farko, yayin da ya yi canjaras sau daya kuma ya shan kashi daya.

A fagen MMA kuwa, Cédric Doumbe da ke da tushe da kamaru ya cire wa kansa kitse a wuta watanni biyu bayan kaye da ya sha a hannun Baki, inda a wannan  karon ya mamaye dan Amurka Jaleel Willis na kotufo tun a turmin farko, lamarin da ya sa alkalin wasa ya dakatar da fafatawar bayan 3 min da dakika 33 da farawa.